Arsenal da Tottenham sun tashi wasa 1-1

Arsenal da Tottenham sun tashi wasa kunnen
doki 1-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da
suka fafata a Emirates a ranar Lahadi.
Arsenal ce ta fara cin kwallo, bayan da Mesut
Ozil ya yi bugun tazara Kevin Wimmer ya ci gida
wato Tottenham.
Tottenham ta farke ta hannun Harry Kane a
bugun fenariti, bayan da Koscielny ya yi wa
Mousa Dembele keta a da'ira ta 18.
Da wannan sakamakon Arsenal ta koma mataki
na uku, yayin da Tottenham ta koma matsayi na
biyar a kan teburin na Premier bayan da suka yi
wasanni 11 a gasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Arsenal da Tottenham sun tashi wasa 1-1"

Post a Comment