Ba ma yin sihiri a fadar shugaban kasa— Geun-hye

An gudanar da zanga-zanga mafi girma a
shekaru masu yawa a birnin Seoul na kasar
Korea ta Kudu, inda masu zanga-zangar suka
bukaci shugabar kasar Park Geun-hye da ta yi
murabus.
Wadanda suka shirya ta, sun ce mutane dubu
dari biyu ne suka fito aka yi zanga-zangar ta
lumana da su, koda yake 'yan sanda sun ce
yawan mutanen bai kai haka ba.
Masu zanga-zangar sun nuna damuwa ne akan
zarge-zargen da ake yi kan yadda shugabar ta
bar wani abokinta na kud-da-kud, wanda bai da
mukamin komai a gwamnatin kasar, amma ake
yin yadda yake so da wasu manufofin kasar.
A Jiya Juma'a, shugabar ta ba jama'a hakuri,
sannan ta musanta zargin cewa an mata asiri ne,
ko kuma tana yin tsafi a fadar shugaban kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ba ma yin sihiri a fadar shugaban kasa— Geun-hye"

Post a Comment