HANKAKA DA KURTATTAKI

Wata rana kurtattaki na koto a gonar wani
bakauye, suna tone shukar da ya yi suna
cinyewa, sai ga hankaka ya zo zai wuce. Ya ce
musu, “Na hore ku da ku tone abin da manomin
nan ke shukawa duka ku cinye.” Sai suka
tambaye shi me yake shukawa. Hankaka ya
amsa musu, “Irin rama.” Kurtattaki suka kada
fiffike suna yi wa hankaka dariya, “Me za mu yi
da irin rama ga dawa da gero.” Kwanci tashi
rama ta fito har ta girma. Manomi ya cire ta ya
kware bawon ya yi zare. Da zaren rama ya tufka
raga wadda ya kafa tarko cikin gonarsa,
kurtattakin nan duka suka fada cikin tarkon. Suna
cikin kici-kicin yadda za su yi su kubuta sai ga
hankaka. Ya dube su ya ce, “Ashe ban gaya
muku ku tone irin ramar nan ba tun kafin ya fito?
Ga abin da nake yi muku gudu nan!” Manomi ya
kama kurtattaki ya kashe, da ma sun addabe shi
da barna. Hankaka ya wuce yana cewa, “KU
KAWAR DA MUGUN IRI, KO YA GIRMA YA
KAWAR DA KU!”

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "HANKAKA DA KURTATTAKI"

Post a Comment