China : Ana kokarin ceto yaron da ya fada rijiya.

Masu aikin ceto a kasar China sun shafe
kwanaki suna kokarin zakulo karamin yaron da
ya fada cikin wata tsohuwar rijiya.
Tun a ranar Lahadi ne yaron mai shekaru biyar
ya fada cikin tsohuwar rijiyar da ta kafe, mai
zurfin mita 40 a yankin Baoding dake Lardin
Hebei.
Mahaifinsa ya shaidawa kafar yada labaran kasar
Chinar cewa, yaron na taya shi tsinkar ganyyaye
ne a gona, lokacin da lamarin ya faru.
Masu aikin ceton na ta amfani da motocin haka
60 da manyan motocin daukar kasa 100 wajen
binciko yaron.
Har yanzu ba a san halin da yake ciki ba, amma
ana aike masa da iskar shaka, da ruwa, da kuma
abinci.
Rijiyar ta yi tsananin tsukewar da ke da matukar
wahala wani babba ya shiga.
Bayan shafe kwanakin da aka yi ana haka, masu
aikin ceton sun iya kai wa da mita 13 ne kawai
zuwa kan wani karfe da a koda yaushe ka iya
ruftawa,
Rijiyar ta shafe shekaru biyar ba a amfani da ita,
kuma ba a saka wata alama dake nuna a yi
hattara ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "China : Ana kokarin ceto yaron da ya fada rijiya."

Post a Comment