Barca ta kalubalanci katin da aka bai wa Messi

Kungiyar Barcelona ta daukaka kara game da
katin gargadi da aka bai wa Lionel Messi saboda
ya bata lokaci yayin wasan da suka ci Sevilla
2-1 a gasar La Liga ranar Lahadi.
An bai wa Messi katin gargadin ne bayan da ya
yi kokarin mayar da takalminsa da ya fice daga
kafarsa sakamakon karo da ya yi da dan kwallon
Sevilla Steven N'Zonzi, bayan dawowa daga hutu.
Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya ce igiyar
daure takalmin dan wasan ce ta tsinke.
A wasan ne Messi ya ci wa Barcelona kwallo na
500 a tarihi, tun lokacin da ya koma can da
murza leda.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Barca ta kalubalanci katin da aka bai wa Messi"

Post a Comment