Ina so na yi aure amma... - Hadiza Gabon

Shahararriyar 'yar fim din Kannywood din nan,
Hadiza Gabon, ta ce tana so ta yi aure amma
lokaci ne kawai bai yi ba.
Da take hira da BBC, Hadiza ta ce aure lokaci
ne, kuma kamar mutuwa, idan Allah ya kawo shi
babu yadda mutum zai guje masa.
"Wallahi babu wata mace da za ta so ta kai
lokacin aure amma ta ki yi" inji Gabon.
Jarumar, wacce ta lashe kyautar 'yar wasan da
ta fi tallafawa babban jarumi a fim ta Africa
Films Awards na bana, ta ce tana kaunar duk
masu goyon bayanta.
Hadiza Gabon, ta ce babu wacce za ta so ta
rinka kaiwa-tana-komowa a gaban iyayenta ba
tare da ta yi aure ba, alhalin kuma ta kai
munzalin yin hakan.
A hirar da Ahmed Abba Abdullahi ya yi da ita da
kuma Ali Nuhu, jarumar ta yi kira ga masu
kaunarta da su yi mata addu'a.
Ta kara da cewa duk wata 'yar fim "da ka gani,
to wallahi tana so ta yi aure".
Muna so mu yi, amma babu yadda muka iya
saboda ba za mu auri kanmu ba.
"A don haka addu'a muke nema daga wurinku," a
cewarta.
Ana sa bangaren Ali Nuhu ya yaba yadda
jarumar ta koyi harshen Hausa da Turanci, da
kuma irin rawar da take takawa a fim.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ina so na yi aure amma... - Hadiza Gabon"

Post a Comment