Kano Pillars ta nada Ikhana sabon kociyanta

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta nada
Khadiri Ikhana a matsayin wanda zai horar da
'yan wasanta.
Kano Pillars da Ikhana sun kulla yarjejeniyar yin
aiki ta shekara daya, daga baya su sake
tattaunawa idan tafiyar ta yi kyau.
Ikhana zai maye gurbin Baba Ganaru wanda ya yi
murabus bayan kammala gasar Firimiyar bana,
yanzu ya koma horar da Wikki Tourists ta
Bauchi.
Wannan ne karo na hudu da Ikhana zai ja
ragamar Pillars, bayan da ya yi a 1991 da
1997/98 da 2007/08,
Ikhana tsohon kociyan Enyimba ya koma aiki da
Pillars daga Shooting Stars.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kano Pillars ta nada Ikhana sabon kociyanta"

Post a Comment