Dole Manchester City ta sauya wasa - Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dole
ne su inganta wasan da suke yi a kusa da
ragarsu domin hana yin asarar maki a gasar
Premier.
City da Middlesbrough sun raba maki daya da
daya a tsakaninsu, bayan da suka tashi wasan da
ci1-1 a fafatwar da suka yi a Ettihad.
Hakan ya bai wa Chelsea damar yin gaba da su
inda ta zama ta daya a kan tebirin gasar.
'Yan wasan City sun rike kwallo har kashi 71 a
wasan, sannan suka dirka kwallon sau 25
sabanin Middlesbrough da suka dirka kwallo sau
biyar, amma duk da haka sun gaza yin nasara a
karo na uku a jere a gidansu.
Guardiola ya ce, "Muna bukatar samun daidaito,
amma ba a samun hakan a kusa da ragarmu."
City ce ta fara cin kwallo ta hannu Sergio Aguero
-- wadda ta zame kwallonsa ta 150 da ya ci wa
kungiyar tun lokacin da ya fara taka mata leda.
Sai dai Middlesbrough ta farke ta hannun De
Roon ana daf da tashi daga wasan.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dole Manchester City ta sauya wasa - Guardiola"

Post a Comment