Manchester City ta ci Barcelona 3-1

Manchester City ta doke Barcelona da ci 3-1 a
gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a
ranar Talata a Ettihad.
Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Lionel
Messi minti na 21 da fara wasa.
Sauran minti shida a je hutu ne City ta farke ta
hannun Ilkay Gundogan, Kevin de Bruyne ya ci ta
biyu bayan da aka dawo daga hutu, sannan Ilkay
Gundogan ya ci ta uku kuma ta biyu da ya ci a
karawar.
Da wannan sakamakon, Barcelona ta ci gaba da
zama a mataki na daya a kan teburin rukuni na
uku da maki tara, yayin da City ke matsayi na
biyu da maki bakwai.
Borussia Monchengladbach wadda ta tashi
kunnen doki 1-1 da Celtic a wasa na biyu na
cikin rukuni, tana mataki na uku da maki hudu
sai Celtic mai maki biyu.
Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:
Besiktas 1 vs Napoli 1
Basel 1 vs Paris St G 2
Ludogorez 2 vs Arsenal 3
Benfica 1 Dynamo Kiev 0
Atl Madrid 2 vs FC Rostov 1
PSV Eindhoven 1 vs Bayern Munich 2

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Manchester City ta ci Barcelona 3-1"

Post a Comment