Man City da Middlesbrough sun tashi wasa 1-1

Manchester City da Middlesbrough sun raba
maki daya da daya a tsakaninsu, bayan da suka
tashi wasan Premier 1-1 a gasar mako na 11 da
suka kara a Ettihad.
City ce ta fara cin kwallo ta hannu Sergio Aguero
kuma ta 150 da ya ci wa kungiyar tun lokacin da
ya koma can da taka-leda.
Daf da za a tashi daga fafatawar Boro ta farke
ta hannun De Roon.
Da wannan sakamakon City ta hada maki 24,
yayin da Boro ke da maki 11.
City za ta ziyarci Crystal Palace a wasan mako
na 12, ita kuwa Boro za ta karbi bakuncin
Chelsea ne.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Man City da Middlesbrough sun tashi wasa 1-1"

Post a Comment