Andy Murray ya dare mataki na daya a Tennis

Andy Murray zai hau mataki na daya a karon
farko a jerin wadanda suke kan gaba a gasar
kwallon tennis a duniya.
Murray ya samu wannan damar ce, bayan da
Milos Raonic ya ce ba zai iya buga wasan daf da
karshe ba da shi a ranar Asabar a gasar
kwararru a Paris, sakamakon raunin da ya yi.
Tun farko Murray na bukatar kai wa wasan
karshe a gasar ta Paris, bayan da wanda ke
matsayi na daya Novak Djokovic ya kasa kai
bantensa a ranar Juma'a.
Tun kafin ranar Asabar Raonic ya ce ba zai iya
buga wasan daf da karshe ba a ranar Asabar
saboda raunin da ya yi, hakan ne ya sa Murray
ya kai wasan karshe a gasar.
Murray zai zama dan wasan tennis na farko dan
Birtaniya da ya taka wannan matsayin tun
lokacin da hukumar tennis ta fara fitar da
jadawalin wadanda suke kan gaba a wasan a
1973.
A kakar bana Murray ya kai wasannin karshe sau
11 a karawa 12, inda ya ci wasanni 73 a kakar
kwallon tennis ta bana.
A ranar Litinin za a bayyana shi a mataki na
daya, a lokacin da hukumar za ta fitar da
jadawalin wadanda suke kan gaba a iya wasan a
duniya,

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Andy Murray ya dare mataki na daya a Tennis"

Post a Comment