Ronaldo zai sa hannu kan ci gaba da wasa a Real Madrid a ranar Litinin

Cristiano Ronaldo ya amince zai saka hannu kan
yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Real
Madrid har zuwa kakar wasan 2021 a ranar
Litinin.
Tun farko kwantiragin Ronaldo mai shekara 31,
da Madrid za ta kare a watan Yunin 2018, idan
ya tsawaita zamansa a kungiyar, za ta cika a
lokacin da ya kai shekara 36.
Ana kuma rade-radin cewar dan wasan tawagar
Portugal zai karbi albashin da zai kai fam
365,000 a kowanne mako.
Ronaldo ya ci kwallaye 371 tun lokacin da ya
koma Madrid da taka-leda daga Manchester
United a shekarar 2009.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ronaldo zai sa hannu kan ci gaba da wasa a Real Madrid a ranar Litinin"

Post a Comment