Messi ya ci kwallaye 500 a Barcelona

Lionel Messi ya ci kwallo ta 500 a Barcelona a
ranar Lahadi a wasan da suka doke Sevilla 2-1 a
ranar Lahadi a gasar La Liga wasan mako na 11
da suka yi.
Messi mai shekara 29, ya ci wa Barca kwallaye
500 a wasanni 592 da ya buga mata tamaula,
ciki har da wasannin sada zumunta.
Dan wasan ya fara ci wa Barcelona kwallo a
cikin watan Mayun 2005, a lokacin yana da
shekara 17.
Yanzu haka dan kwallon na Argentina ya bai wa
Paulino Alcantara tazarar kwallaye 105, wanda
ya rike matsayin dan wasan da ya fi ci wa
kungiyar kwallaye a shekarar 1912 da 1927.
A cikin watan Afirilu ya ci kwallo na 500 a
wasannin da ya buga wa kasarsa da Barcelona a
karawar da suka ci Valencia 2-1.
Messi ya zura kwallaye 320 a manyan wasannin
Spaniya da kuma 90 da ya ci a gasar cin kofin
zakarun Turai, sauran ya ci su ne a Uefa Super
Cup da gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Messi ya ci kwallaye 500 a Barcelona"

Post a Comment