Sanchez ya yi rauni a wajen atisaye

Dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez, ya yi rauni
a lokacin da yake yin atisaye a tawagar kwallon
kafa ta Chile.
Sanchez mai shekara 27, ba zai buga wa Chile
wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi
da Colombia a ranar Alhamis ba.
Sai dai likitocin tawagar Chile sun ce, dan
kwallon zai iya murmurewa ya kuma buga wa
kasar karawar da za ta karbi bakuncin Uruguay a
ranar Talata.
Sanchez wanda ya ci wa Arsenal kwallaye
takwas a kakar wasannin bana, ya buga wa
kungiyar wasan da ta yi kunnen doki 1-1 da
Tottenham a ranar Lahadi a gasar Premier.
Arsenal wadda ke mataki na hudu a kan teburin
Premier, za ta ziyarci Manchester United a ranar
19 ga watan Nuwamba a gasar Premier
wasannin mako na 12.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sanchez ya yi rauni a wajen atisaye"

Post a Comment