Clinton: Trump ya zargi FBI da taimaka wa magudi

Donald Trump ya soki hukumar FBI saboda
cewar da ta yi Hillary Clinton ba za ta gurfana
gaban kotu ba kan sabbin sakonnin e-mail dinta
da hukumar ke bincike a kai.
Mr. Trump ya shaidawa wani gangamin yakin
neman zabensa a jihar Michigan cewa hukumar
ba za ta iya yin nazari kan sakonni e-mail
650,000 ba a cikin kwannaki takwas kawai, in da
ya kara da Mrs Clinton na samun kariya ne daga
gwamnatin da ke goyon bayan magudi.
Kalaman nasa dai sun zo ne jim kadan bayan
shugaban hukumar ta FBI, James Comey ya aike
da wata wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar
cewa matsayin hukumarsa bai canza ba daga
wanda ta cimma a watan Yuli cewa ba a samu
wani abin zargi ba a sakonnin na e-mail.
''Mun ga wasikar da Daraktan FBI Comey ya aike
wa majalisar dokoki. Mun ji dadi da cewa ya
kara tabbatar da matsayar da suka cimma a
watan Yuli. Muna farin ciki cewa an warware
wannan matsalar.'' In ji mai magana da yawun
ofishin kamfe din Mrs Clinton, Jennifer Palmeiri.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Clinton: Trump ya zargi FBI da taimaka wa magudi"

Post a Comment