Zaben Amurka: Donald Trump ya kai kara kotu

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar
Republican, Donald Trump, ya shigar da karar
wani jami'in zabe a jihar Nevada, yana zargin
cewa an bar rumfar zabe a bude fiye da lokacin
da aka tsara.
Sai dai alkalin kotun, Gloria Sturman, ya yi watsi
da karar, bisa la'akari da hadarin da ke tattare da
bayyana sunayen masu aikin zabe.
Lauyoyin Mista Trump sun nemi ka da a hada
takardun zaben da aka kada da wuri da na
lokacin zabe na bai daya.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a a jihar Nevada ta nuna
cewa 'yan takarar biyu na tafiya kan-kan-kan.
Rahotanni daga sassan kasar da dama sun ce
jama'a sun fito sosai domin kada kuri'unsu, inda
aka kafa dogayen layuka.
Dukkansu sun yi kokarin jan hankalin masu kada
kuri'a a jihohin da ake ganin takarar ta fi zafi da
suka hada da North Carolina da Pennsylvania da
Michigan.
Hillary Clinton ta nemi jama'a da su nuna karfin
zuciya, yayin da shi kuma Trump ya ce
Amurkawa na da damar kawar da tsarin da ya
"daurewa cin hanci gindi".
Misis Clinton dai na gaban Mista Trump da maki
hudu kacal, a kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wanda
ya fi farin jini.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zaben Amurka: Donald Trump ya kai kara kotu"

Post a Comment