Hare-haren IS sun halaka mutane 21 a Iraki

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai wasu hare-haren
kunar bakin wake biyu a biranen Tikrit da
Samarra na Iraki, inda ta kashe akalla mutane
21.
An kai dukkan hare-haren ne ta yin amfani da
motocin daukar marasa lafiya da aka shake su
da bama-bamai.
An tayar da daya daga cikin bama-baman ne a
kan layin motocin dake jira a bincike su a wurin
duba ababen hawa a Tikrit.
Shi kuma harin na Samarra, an kai shi ne a wurin
da ake ajiye motoci da masu ibada 'yan shi'a ke
amfani da shi.
Jami'ai sun ce 10 daga cikin wadanda suka
mutun 'yan kasar Iran ne.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hare-haren IS sun halaka mutane 21 a Iraki"

Post a Comment