Chelsea ta dare kan teburin Premier

Chelsea ta shararawa Everton kwallaye 5-0 a
gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata
a Stamford Bridge.
Eden Hazard ne ya fara cin kwallo, sannan
Marcos Alonso ya ci biyu, kuma daf da za a je
hutun rabin lokaci Diego Costa ya kara ta uku.
Bayan da aka dawo daga hutu ne, Eden Hazard
ya kara ta hudu kuma ta biyu da ya ci a karawar,
daga karshe Pedro ya ci ta biyar.
Da wanana sakamakon Chelsea wadda ta yi
wasanni 11 ta koma mataki na daya a kan
teburin Premier da maki 25.
Chelsea za ta buga wasan gaba ne da
Middlesbrough, yayin da Everton za ta karbi
bakuncin Swansea City a wasannin mako na 12 a
gasar ta Premier.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Chelsea ta dare kan teburin Premier"

Post a Comment