Hillary Clinton ba ta da laifi in ji hukumar FBI 7 Nuwam

Daraktan hukumar FBI ya ce bayan nazari a kan
sabbin sakonnin emails din da aka gano na
Hillary Clinton a lokacin da ta ke matsayin
sakatariyar harkokin wajen Amurka, hukumar na
nan kan ra'ayinta na farko cewa ba za a gurfanar
da ita gaban kuliya ba.
Kwanaki biyu kafin zaben shugaban kasar da za
a yi, James Comey ya aike da wasika ga
majalisar dokokin kasar in da ya ce hukumar ta
FBI ba ta canja matsayarta ta watannin baya ba
cewa Mrs Clinton ba tayi laifi ba wajen
ta'ammali da bayanan sirri.
A makon da ya gabata ne dai yakin neman zaben
Mrs Clinton ya shiga rudani bayan da Mr Comey
ya ce jami'an hukumar sa za su sake nazari a
kan sakonnin ta na email.
Jam'iyyar Democrats ta ce wannan sanarwa ta
zo a makare ta yadda hukumar FBI din ba zata
iya goge bata sunan da ta yiwa Mrs Clinton ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hillary Clinton ba ta da laifi in ji hukumar FBI 7 Nuwam"

Post a Comment