Gwamnati ta yi lugudan wuta kan Musulman Rohingya

Gwamnatin Myanmar ta amsa cewa, tayi amfani
da jiragen helikofta na yaki wajen bude wuta a
wasu kauyuka na Musulman Rohingya da basu
da rinjaye a yammacin kasar.
Kafofin watsa labarai na kasar sun ce an bukaci
daukin jiragen yakin ne bayan taho mu gama
tsakanin sojoji da wasu da ake zargi 'yan bindiga
na kabilar Rohingya ne, ta yi sanadin mutuwar
mutane takwas, biyu daga ciki sojoji.
Jihar Rakhine, wacce ta hada iyaka da
Bangledash, wuri ne da 'yan kabilar Rohingya da
dama ke zaune, wadanda ake nuna wa wariya.
Wasu majiyoyi na kabilar Rohingya sun zargi
sojojin kasar da yunkurin kawar da kabilarsu baki
daya, sai dai gwamnatin kasar wacce Aung San
Suu Kyi ke jagoranta, ta ce samamen da aka kai,
wani bangare ne na neman wadanda suka kai
harin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gwamnati ta yi lugudan wuta kan Musulman Rohingya"

Post a Comment