Kwarewar Lukaku ya wuce zama a Everton — Koeman

Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya ce
kwarewar da Romelu Lukaku yake da ita a fagen
murza-leda ya fi karfin ya ci gaba da zama a
kungiyar.
Koeman ya ce "Ina jin Lukaku ya hada komai a
wasan kwallon kafa, ya kware wajen murza leda
ya kuma iya cin kwallo yana da tsawo yana kuma
da karfi".
Kwantiragin Lukaku da Everton za ta kare a
karshen kakar 2019, ya kuma koma kungiyar da
taka-leda ne daga Chelsea, inda yanzu haka ya ci
mata kwallaye 68 a wasanni 137.
Koeman ya kwatanta salon kwallon da Lukaku ke
buga wa da irin wadda tsohon dan kwallon
tawagar Netherlands, Patrick Kluivert ya yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kwarewar Lukaku ya wuce zama a Everton — Koeman"

Post a Comment