Ronaldo zai kara shekara 10 a Real bayan 2021

Cristiano Ronaldo ya ce zai iya ci gaba da taka
leda a kungiyar zuwa shekara 10, idan
yarjejeniyar da ya sake kullawa da kungiyar ta
kare.
Kwantiragin Ronaldo mai shekara 31, da Real
Madrid na shirin karewa a watan Yunin 2018,
amma ya tsawaita ta, inda zai kai karshen kakar
wasan 2021.
Dan kwallon na tawagar Portugal ya ce ba
wannan ba ne karo na karshe da zai tsawaita
yarjejeniyar ci gaba da wasa a Madrid, yana
fatan sai ya kai shekara 41 kafin ya yi ritaya.
Ronaldo ya ci kwallaye 371 tun lokacin da ya
koma Madrid da taka-leda daga Manchester
United a shekarar 2009.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ronaldo zai kara shekara 10 a Real bayan 2021"

Post a Comment